Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, da kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, sun gudanar da wani taron hadin gwiwa a karon farko, domin bunkasa fannonin samar da ababen more rayuwar jama'a.
Yayin taron wanda ya gudana a ranar Laraba, a birnin Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, an cimma matsaya daya ta yarjejeniyar shirin 'daukar matakan hadin kai, a fannonin samar da ababen more rayuwar jama'a, tsakanin ma'aikatar kasuwancin ta Sin da kuma kungiyar AU.
Mai ba da taimako ga ministan kasuwancin Sin Mista Zhang Xiangchen, da mataimakin shugaban kwamitin AU Erastus Mwencha ne suka jagoranci taron cikin hadin gwiwa.
Da yake tsokaci yayin taron Mr. Zhang ya ce, kamfanonin kasar Sin da suka shafi sashen manyan ayyukan samar da ababen more rayuwar jama'a, sun samu kyakkyawan sakamako a fannonin sifiri da jigila, da makamashi, da sadarwa da dai sauransu. Ya ce irin wadannan kamfanoni sun riga sun gudanar da ayyuka a wasu kasashen Afirka. Sabo da haka ana iya ganin kwarewar Sin a fagen bada taimako ga Afirka, a fannonin ayyukan more rayuwar jama'a.
Shi kuwa a nasa bangare Mr. Erastus Mwencha cewa ya yi, ayyukan samar da ababen more rayuwar jama'a suna da muhimmiyar ma'ana ga bunkasar Afirka, kuma kwamitin AU na fatan ganin an inganta hadin gwiwa da Sin a wannan fanni. (Danladi)