Sin na fatan sa kaimi ga yin shawarwari kan daddale yarjejeniyar zuba jari da kungiyar EU, in ji firaministan Sin
A yau Jumma'a 15 ga wata, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari da takwaransa na Holland Mark Rutte, inda ya ce, shugabannin Sin da na kasashen Turai za su gana da juna karo na 16 nan ba da dadewa ba, kuma Sin na fatan yin fasali kan dangantaka da makomar juna bisa manyan tsare-tsare da kungiyar kasashen Turai(EU), da sa kaimi ga yin shawarwari kan daddale yarjejeniyar zuba jari, da kuma karfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Da fatan kasar Holland za ta taka muhimmiyar rawa a wannan fanni a matsayin mambar kungiyar EU.
A nasa bangare, Mark Rutte ya bayyana cewa, Holland tana ganin cewa, duk bangarorin biyu za su ci gajiyar kara saurin sa kaimi ga yin shawarwari kan daddale yarjejeniyar zuba jari da kafa yankin yin cinikayya ba tare da shinge ba tsakanin kasashen Turai da Sin. Don haka yana fatan cewa, ganawa tsakanin shugabannin kasashen Turai da na Sin karo na 16 za ta sami babban sakamako.(Fatima)