Kasar Sin za ta harba sabon nau'in tauraron dan Adam mai ba da jagoranci ga zirga-zirga da ake kira Beidou kafin nan da shekara ta 2015, baya ga fara aikin gwaji kan wasu sabbin fasahohi, da tsare-tsare game da hakan da za ta yi.
Hakan dai na cikin jawabin da Ran Chengqi, shugaban ofishin kula da tsare-tsaren jagorancin zirga-zirgar taurarin dan Adam na kasar Sin ya gabatar, yayin bikin bude taron shekara-shekara karo na biyar, kan ilimin ba da jagorancin zirga-zirgar taurarin dan Adam na kasar Sin, wanda aka fara a birnin Nanjing.
A ta bakin Mr. Ran, kasar Sin za ta shiga tsarin hadakar ayyukan taurarin dan Adam a lokacin da ya dace, domin kara azama ga aikin raya tsarin jagorancin zirga-zirgar tauraron dan Adam na Beidou a duk duniya.
Kaza lika Mr. Ran ya ce za a yi kokari wajen ganin an fara ba da hidima game da wannan aiki kafin shiga shekarar ta 2015.(Kande Gao)