in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu nasarar harba tauraron dan Adam mai lura da harkokin sufuri mai suna Beidou karo na 10
2011-12-02 15:13:23 cri
Da misalin minti 7da karfe 5 na safiyar ranar Jumma'ar nan 2 ga wata, a cibiyar harba taurarin dan Adam ta Xichang dake kasar Sin, an samu nasarar harba tauraron dan Adam mai lura da harkokin sufuri mai suna Beidou a karo na 10.

Harba tauraron cikin nasara a wannan karo ya shaida cewa, an samu muhimmin ci gaba wajen raya tsarin taurarin dan Adam masu lura da harkokin sufuri na Beidou na kasar Sin. A halin yanzu, an kusan kammala aikin gina wannan tsari, kuma kafin karshen shekarar da muke ciki, zai fara aikin bada taimako ga harkokin sufuri da sauransu a kasar Sin da sauran yankuna, a kokarin biyan bukatun jama'a a fannonin sufuri, aikin kamun kafi, harkokin gandun daji, hasashen yanayi, sadarwa da sauransu.

An ce, kafin karshen shekara mai kamawa, kasar Sin za ta kara harba irin wadannan taurarin dan Adam masu lura da harkokin sufuri, da fadada yankunan da taurarin za su shafa, a kokarin kara samar da hidima mai kyau a fannin sufuri da sauransu.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China