in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta cimma nasarar harba wani sabon tauraron dan Adam
2012-10-26 09:56:12 cri

Jiya Alhamis 25 ga wata da karfe 23 da minti 33, a cibiyar harba kumbo dake birnin Xichang na kasar Sin ne aka cimma nasarar harba tauraron dan Adam mai ba da jagoranci a fannoni da suka shafi zirga-zirga mai suna "Bei Dou" ta hanyar yin amfani da roka mai daukar kumbo ta "Chang Zheng 3".

Wannan tauraron dan Adam zai sadu ne da taurarin dan Adam 15 da aka harba a baya domin kafa wani tsarin gudanar da ayyuka tare. Bisa shirin da aka tsayar, an ce, wannan tsarin bad a jagoranci wajen zirga-zirga zai ba da hidima ga galibin yankunan dake Asiya-Pacific daga farkon shekara mai zuwa.

Anyi hasashen cewa, tsarin tauraran dan Adam na "Bei Dou" da kasar Sin ta gabatar da shi da kanta yana iya gudanar da ayyuka tare da sauran tsare-tsare na kasashen waje. Shi ne ya sa wannan nasara ya zama wani muhimmin mataki ga kasar Sin a fannin tsaron kasar, raya tattalin arziki da kuma al'umma. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China