A ranar 30 ga wannan wata da safe, da misalin karfe hudu da minti 50, kasar Sin ta yi amfani da roka wajen harba wasu taurarin Adam guda biyu na kula da harkokin sufuri, taurarin da suka shiga hanyar da aka tsara kamar yadda ya kamata.
Wannan shi ne na farko da kasar Sin ta harba taurari biyu da roka guda a lokaci daya. Taurarin sun kasance na 12 da na 13 cikin tsarin taurarin kula da harkokin zirga-zirga da ake kira Beidou. Yadda aka harba su cikin nasara na da muhimmiyar ma'ana musamman ta bangaren kyautata aikin kula da harkokin sufuri a fadin da tsarin ke shafa.
An ce, tun bayan da aka fara gwajin gudanar da tsarin a ranar 27 ga watan Disamban shekarar bara, an kuma fadada ayyukan tsarin zuwa fannonin sufuri, yanayi, kamun kifi, sadarwa, ban ruwa, safiyo da dai sauransu.
A shekarar bana Sin za ta kara harba wasu taurarin dan Adam guda uku da za su shiga cikin tsarin na Beidou, don kara inganta aikin wannan shiri da kuma fadada yankin da tsarin zai iya shafa.(Lubabatu)