A dai wannan rana, babbar kungiyar kula da harkokin aikin haji ta Sin da kuma karamin ofishin jakadan kasar Sin a birnin Jeddah na Saudiya, sun shirya wani taron manema labarai tare, inda suka bayyana halin da ake ciki, dangane da shirin aikin haji, na maniyyatan kasar ta Sin.
Mr. Hong Changyou ya ce, a bana, yawan mutanen da za su yi aikin haji daga kasar ta Sin, ya yi daidai da na shekarar bara, inda yawan su ya kai dubu 13 da dari 8, don haka, shekarar ta zama daya daga cikin shekarun da suka fi samun maniyyata aikin hajin a tarihi.
Yawa-yawan maniyyatan dai sun fito ne daga larduna, birane da kuma yankuna masu cin gashin kansu guda 26 na kasar ta Sin. A yanzu dai, maniyyatan na sauka ne a birnin Makka, kuma za su koma gida daga birnin Jeddah bayan kammala aikin hajin bana.(Maryam)