in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da kasashe masu bin addinin Musulunci sun kara yin hadin gwiwa
2012-07-15 17:25:54 cri
A kwanan baya, an yi taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashe masu bin addinin Musulunci karo na 6. Wannan taro shi ne da a kan shirya a lokacin da ake shirya bikin baje kolin kayayyakin abinci na halal a lardin Qinghai, inda batun tabbatar da kayayyakin abinci na halal ya zama batun da ya fi jawo hankulan mahalarta taron.

Wanda yake kula da cibiyar shirya taruruka da bukukuwa na Sharjah na tarayyar sarkunan Arabiya ya ce, yanzu yawan kayayyakin abincin da ake shigar da su zuwa yankin Gabas ta tsakiya ya kai kashi 80 cikin kashi dari, kayayyakin abinci suna da kasuwa kwarai. Idan kamfanonin samar da kayayyaki abinci na halal na kasar Sin suna son samun karbuwa a kasuwannin Gabas ta tsakiya, dole ne suna bukatar yin kokari wajen tallace-tallace, kintsawa da dai sauransu.

A yayin taron, Mr. Shao Yong, shugaban kamfanin Keke Xili na lardin Qinghai, wato kamfani mafi girma wajen sarrafa naman shanu na Tibet a kasar Sin ya bayyana cewa, a matsayin wani mamban dake samar da kayayyakin abincin halal, kamfaninsa yana fatan zai iya kara yin hadin gwiwa da 'yan kasuwa na kasashe da yankuna masu bin addnin Musulunci wajen saya da sayar da kayayyakin abinci bisa ka'idar yada al'adun kayayyakin abinci na musulmai a kokarin cimma moriyar juna da samun ci gaba tare.

An labarta cewa, tun daga shekara ta 2007, ake shirya taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashe masu bin addinin Musulunci a kowace shekara. Sabili da haka, yanzu dandalin ya zama wani muhimmin dandali wajen bunkasa da kara yin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashe masu bin addinin Musulunci a fannin tattalin arziki da cinikayya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China