in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron wakilan musulmin kasar Sin karo na 9 a birnin Beijing
2011-09-13 17:33:02 cri
A ranar 13 ga wata da safe, an bude taron wakilan musulmin kasar Sin karo na 9 wanda za a shafe tsawon kwanaki uku ana yinsa a nan birnin Beijing, kuma wakilan musulmin kasar Sin 'yan kabilu daban daban 354 suke halartar taron.

A gun taron, za a duba rahoton aiki na kwamitin kungiyar kula da harkokin musulunci ta kasar Sin da kuma tsarin ka'idojin kungiyar, tare kuma da tabbatar da tambarin kungiyar da zaben sabon kwamitin kungiyar da shugabanninta.

An kafa kungiyar kula da harkokin musulunci ta kasar Sin a shekarar 1953, kungiyar da ta kasance kungiyar Islama ta farko da ta shafi duk fadin kasar Sin a tarihin kasar.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China