Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhai Jun ya halarci bikin bude taron, inda ya bayyana cewa, wayewar kai ta kasar Sin da ta kasashen da ke bin addinin Musulunci na da daddaden tarihi, kuma sun yi koyi da juna yayin da suke kokarin raya kasa, kuma akwai dangantakar sada zumunci cikin jituwa tsakaninsu, kuma irin dangantakar da ke tsakaninsu ta zama abin misali wajen yin mu'amala tsakanin wayewar kai daban daban a duniya. Yanzu, ana girmama mutane masu bin addinin musulunci sama da miliyan 20 a fannin al'adu da addini da zaman rayuwarsu a kasar Sin, su ma sun ba da babbar gudummawa wajen ingiza zaman lafiya da lumana da wadata tsakanin al'umomi daban daban a kasar Sin.
Sakatare janar na kungiyar hadin gwiwa kan kasashen da ke bin addinin Musulunci ta OIC Ekmeleddin Ihsanoglu ya yi jawabi, inda ya bayyana cewa, Sin ta dade tana mu'amala da kasashen da ke bin addinin Musulunci, kuma bangarorin biyu sun samu ci gaba ta mu'amala tsakaninsu, ya yi imani cewa, dangantakar sada zumunta da ke tsakanin kasar Sin da kungiyar OIC za ta samu bunkasuwa.(Bako)