Haka zalika, Wang Yi ya kara da cewa, ziyarar da shugaban kasar Rasha zai kawo wa kasar Sin, na da muhimmiyar ma'ana wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a yanzu da kuma nan gaba.
Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da dukufa wajen zurfafa fahimtar juna bisa fannoni daban daban, da kuma ciyar da hadin gwiwar kasashen biyu gaba yadda ya kamata, don inganta hadin gwiwa da fahimtar kasashen biyu kan harkokin MDD, da dai sauran harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a iya ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare gaba.
A nasa bangare, Mr. Lavrov ya nuna cewa, kasar Rasha na mai da hankali sosai kan ziyarar da shugaba Putin zai yi a kasar Sin, kuma za ta dukufa tare da kasar Sin, wajen samun sakamako mai gamsarwa a yayin ziyararsa a kasar Sin.
Bugu da kari, manyan jami'an biyu sun kuma yi musayar ra'ayi kan wasu harkokin dake janyon hankulan kasashensu. (Maryam)