Shugabannin kungiyar G7 sun kuma nuna yabo ga kokakin da kasar Ukraine ta yi wajen sassauta da magance tashe tashen hankali a cikin kasar, tare da yin allah wadai da kasar Rasha game da rashin cika alkawarinta kan yarjejeniyar da aka cimma a birnin Geneva kan batun Ukraine, maimakon haka ma a cewar G7, kasar Rasha ta kara ruwa wutar tashe tashen hankali a wasu yankunan kasar Ukraine, da kuma gudanar da atisayen soja a kan iyaka da Ukraine.
Bugu da kari, shugabannin kungiyar sun bayyana cewa, a shirye suke na kara kakaba wa kasar Rasha karin takunkumi, amma duk da haka suna fatan warware wannan rikici ta hanyar sulhu. (Maryam)