in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta gargadi Ukraine game da yunkurin shiga kungiyar tsaro ta NATO
2014-04-20 17:16:13 cri
Kakakin shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov ya ce kasar Rasha ba za ta amince Ukraine ta shiga kungiyar tsaro ta NATO ba.

Ya ce NATO kungiyar tsaro ce ta soji, wadda idan har kasar Ukraine ta shiga cikinta, NATOn za ta kara yawan tasirinta a yankunan dake iyaka da Rasha, lamarin da kuma ka iya canja tsarin tsaron kasashen Turai, tare da haddasa barazana mai tsanani ga kasar Rasha.

Wannan dalili a cewar Peskov ya sa ya wajaba kasar Rasha ta dauki matakai kan kasar Ukaraine a matsayin kariyar kai, muddin dai Ukraine din ta kuskura ta shiga kawancen kungiyar ta NATO.

Dmitry Peskov ya kara da cewa, kasar Rasha ta riga ta tsara shirye-shirye da dama, don magance ci gaba da yaduwar tashe-tashen hankula a gabashin kasar Ukraine. Ya ce, dalilin da ya haddasa irin wadancan tashe-tashen hankula shi ne, karancin amincewa juna tsakain jama'ar yankunan dame da jagorancin Kiev.

Ya ce jama'ar Ukraine ne ke da ikon warware matsalolin da ke fuskantar su ta hanyar da ta dace, maimakon kasar Amurka, da Rasha ko kungiyar tarayyar kasashen Turai.

Bugu da kari, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a wannan rana cewa, kasarsa ba ta burin ganin tabarbarewar tattalin arzikin kasar Ukraine, ba kuma ta fatan ganin kasashen Turai sun nuna shakku game da aikin sarrafa iskar gas wanda ya shafi kasar. Ya ce hana Ukraine shiga kungiyar NATO ba shi da alaka da halin siyasar Ukraine, ko batun babban zaben kasar da ke tafe a ranar 25 ga watan Mayu mai zuwa.

Kaza lika shugaba Putin ya yi kira ga kasashen Turai, da su ba da taimako wajen farfado da tattalin arzikin kasar Ukraine, ta yadda kasar Rasha za ta iya ci gaba da samar da iskar gas ga kasashen Turai.

Game da batun ko kasar Rasha za ta iya kyautata dangantakar dake tsakaninta da wasu kasashen yammacin duniya nan da karshen shekarar bana kuwa, shugaba Putin ya bayyana cewa, tattaunawa tsakanin kasar Rasha da kasashen yammacin duniya na ci gaba yadda ya kamata, nasarar hakan kuma ta dogara ga aniyar kasashen na yamma a maimakon kasar ta Rasha.

Daga nan sai ya bayyana kasashen yammacin duniya a matsayin abokan Rasha, wadanda babu wani abu da zai hada dangantakarsu da Rasha kara farfado yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China