in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen Sin da Rasha sun yi musayar ra'ayoyi kan taron Geneva karo na 2
2014-01-22 12:38:53 cri
A ranar 21 ga wata da dare, a birnin Montreux da ke kasar Switzerland ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov.

Bangarorin biyu sun kuma yi musayar ra'ayi game da taron birnin Geneva karo na biyu game da Siriya. Wang Yi ya ce, jiya kasar Sin ta bayyana shawarwari biyar da take ganin za su taimakawa wajen warware batun Siriya. Yanzu abu mai muhimmanci shi ne a gaggauta tsagaita bude wuta da kawo karshen tashe-tashen hankali, kuma da farko ya kamata a cimma ra'ayi guda game da tsarin da za a bi na yin shawarwarin da kuma tsari na bin diddigin shawarwari, don kada a yi kasala a kokarin da ake na yin shawarwarin.

Lavrov ya ce, kasashen Rasha da Sin suna da ra'ayi guda game da batun Siriya, kuma za su ci gaba da tuntubar juna.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China