A yayin tattaunawar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi maraba sosai ga shirin yarjejeniyar da kasashen Rasha da Amurka, suka cimma game da batun makamai masu guba na Syria, tana kuma fatan za a aiwatar da abubuwan dake cikin yarjejeniyar.
Bugu da kari Wang Yi ya ce, kasar Sin na ganin cewa, ba za a iya warware matsalar da kasar Syria ke fuskanta, ta hanyar daukar matakin soja ba. Yace Kasar Sin na fatan ci gaba da taka muhimmiyar rawa, a fagen inganta yunkurin da ake yi na warware matsalar Syria a siyasance.
A nasa bangaren, Lavrov ya amince da wannan matsayi na kasar Sin. Bugu da kari bangarorin biyu sun amince da ci gaba, da yin hadin gwiwa tsakaninsu. (Bilkisu)