Shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen biyu su fahimci tasirin da dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha ta yiwa dukkan duniya, da nuna goyon baya ga juna da kuma kara yin mu'amalar fasahohin gudanar da ayyukan kasa a tsakaninsu. Kana kasashen biyu su kara aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito bisa bukatun raya dangantakarsu a sabon halin da ake ciki don inganta hadin gwiwarsu.
A nasa bangare, Medvedev ya bayyana cewa, kasar Rasha tana son kara yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin tattalin arziki, cinikayya, fasaha, makamashi da dai sauransu, da kara yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa da kuma ayyuka a karkashin tsarin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a inganta dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)