Yayin shawarwarin, firaminista Li ya bayyana cewa, kasar Sin kasa ce mafi girma wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a yankin Asiya, Najeriya ma na daukar matsayin hakan a yankin na Afrika. Saboda haka, karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu na da amfani wajen samar da alheri ga jama'arsu, har ma zai taka rawa wajen bunkasuwar yankunansu da duk duniya baki daya.
A nasa bangaren, shugaba Jonathan ya ce, kasarsa ta yi godiya ga taimako da goyon baya da kasar Sin ke ba ta, da nahiyar Afrika, da kuma kungiyar ECOWAS. Ya ce Najeriya har ila yau ta gamsu sosai kan jawabin da firaminista Li ya gabatar a cibiyar kungiyar AU, wanda ya shafi shirin hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika.
Bayan shawarwarin, shugabannin biyu sun halarci bikin daddale yarjejeniyoyin hadin kai a tsakanin kasashensu a fannonin tattalin arziki, aikin jinya da kiwon lafiya, da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a, sararin samaniya, sha'anin noma da dai sauransu. Sun kuma bayar da hadaddiyar sanarwa tsakanin Sin da Najeriya.
A yayin taron manema labaru da aka shirya bayan shawarwarin, shugabannin biyu sun bayyana anniyarsu bai daya wajen karfafa hadin kai tsakanin kasashen su a fannoni daban daban, musamman ma manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, ciki har da ayyukan layin dogo. (Bilkisu)