in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya yi alkawarin inganta hadin gwiwa da Togo da Mali
2014-05-08 10:03:30 cri

Firaministan kasar Sin dake ziyara a Nigeriya Li Keqiang ya yi alkawarin inganta hadin gwiwwa tsakaninn kasarsa da kasashen Togo da Mali.

Ya yi alkawarin ne lokacin da ya gana da shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe da firaministan kasar Mali Mousa Mara daban daban wadanda suke a Abuja, babban birnin Nigeriya domin hallarta babban taron tattalin arzikin duniya a kan Afrika.

A lokacin ganawarsa da shugaba Gnassingbe, Mr. Li ya ce, Sin tana da niyyar cigaba da inganta zumuncin gargajiya tsakaninta da Togo wanda aka gada tun tsoffin iyayen kasashen biyu, kuma za ta kara azama wajen karfafa wannan abota domin kaiwa ga wani sabon matsayi.

A nasa bangaren, shugaba Gnassingbe ya ce, abota mai tsawo dake tsakanin kasshen biyu yana da kwari sosai, da kuma makoma mai haske. Ya kara da cewa, kasarsa tana fatan inganta wannan dangantaka da Sin a bangarori daban daban, ya kuma ce, ganin yadda kasashen Afrika suke mutuntan zumuncin dake tsakanin Sin da nahiyar wajen kawo zaman lafiya da cigaba, yana matukar goyon bayan tsarin dangantakar sassan biyu da firaminitsan Sin ya yi bayani a kai a cikin jawabinsa a cibiyar kungiyar AU. ya tabbatar da cewa, a shirye suke a matsayin shugabannin kasashen nihiyar su yi aiki da Sin domin habaka dabarun da za'a bi wajen cigaban bangarorin biyu.

A ganawar da ya yi da takwaransa na kasar Mali Mousa Mara, firaminista Li ya sanar da cewa, kasarsa na goyon bayan Mali a kokarinta na kare hakkin mallakarta, hadin kai da 'yancin yankunanta.

Shi ma Mr. Mousa a martaninsa ya yaba bisa ga dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, inda ya ce, tana haifar da alheri matuka. Ya ce, Mali ta amince gaba daya da tsarin dangantakar da Sin ta fitar da ya shafi nahiyar Afrika kamar yadda firaminista Li ya bayyana cikin jawabinsa a cibiyar AU, don haka Malin za ta yi iyakacin kokarinta na ganin an samu sakamako mai armashi da zai amfani Sinawa da al'ummar Afrika. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China