in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya isa birnin Abuja ya fara ziyarar aiki a Nijeriya
2014-05-07 09:00:34 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin Abuja, babban birnin kasar Nijeriya a ranar 6 ga wata da dare, domin fara ziyarar aiki a kasar.

Li Keqiang ya yi nuni da cewa, kasar Nijeriya ta kasance babbar kasa ta farko a fannin tattalin arziki a nahiyar Afirka, kuma wata muhimmiyar abokiyar hadin kai ta kasar Sin. Don haka yana sanya ran yin musanyar ra'ayoyi tare da shugabannin Nijeriya kan dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu da sauran batutuwan da ke jawo hankulansu. Firaminista Li ya ce, yana fatan ta ziyararsa, za a kara inganta zumuncin gargajiya, da tsara shirin hadin kai irin na moriyar juna, da ciyar da dangantakarsu gaba.

A yayin ziyararsa, bisa gayyatar da shugaban dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya Klaus Schwab ya yi masa, Li Keqiang zai halarci cikakken zaman taron koli na Afirka na dandalin karo na 24, inda zai gabatar da jawabi tare da ganawa da wasu shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China