Bayan ziyararsa a kasar Habasha, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya a daren ranar Talata 6 ga wata don fara ziyarar aiki a hukunce. Manyan kamfanonin watsa labaru na Najeriya ciki har da kamfanin dillancin labaru na kasar wato NAN sun mai da hankali sosai kan ziyarar Li a kasar.
A ranar Laraba 7 ga wata, firaminista Li ya gana da shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan. Game da haka, NAN ya bayyana cewa, a gun shawarwarin tsakanin shugabannin, an daddale wasu yarjejeniyoyi da takardun fahimtar juna, ciki har da wata yarjejeniyar taimakon juna a fannin zirga-zirga a sararin sama, wanda hakan zai kara inganta cudanyar jama'ar kasashen biyu, tare da sa kaimi ga mu'ammalarsu a fannin kasuwanci.
Labarin da NAN ya fitar ya ce, firaminista Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana cikakken goyon baya ga mulkin kai da cikakken yankin kasar Nijeriya, tana kuma goyon bayan bunkasuwar tattalin arzikinta, wadanda dai suka kasance burin gwamnatin Nijeriya da jama'arta.
A ranar safiyar Alhamis din nan 8 ga wata, firaminista Li zai halarci cikakken zaman taron koli na Afirka na dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya karo na 24, inda zai gabatar da jawabi. Game da haka, Kamfanin NAN ya yi fatan shugabannin kasashen Afirka za su yi koyi daga nasarorin da kasar Sin ta samu, don raya tattalin arziki da amfanawa jama'arsu. (Danladi)