in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya amince da tayin Amurka na tura mata jami'an tsaro don zakulo 'yan matan da aka sace a Chibok
2014-05-07 20:10:31 cri

Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya amince da wani tayin gwamnatin kasar Amurka na tura jami'an tsaronta zuwa Najeriya don taimakawa zakulo dalibai mata da aka sace a garin Chibok na jihar Borno.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin watsa labarai Dr. Reuben Abati ya bayar a ranar Talata a Abuja, babban birnin tarayya, inda ya ce, shugaba Jonathan ya amice da turo sojojin Amurka a yayin da yake wata tattaunawa ta waya da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a ranar Talata da yamma.

An ce, taimakon da kasar Amurka za ta baiwa Najeriya ya hada da, girke jami'an tsaro da na'urori a garin Chibok, a wani kokari na gudanar da hadin-gwiwa tare da sojojin Najeriya domin gano 'yan matan da aka sace.

Sanarwar ta ce, John Kerry ya tabbatarwa shugaba Jonathan cewa, Amurka za ta yi iyakacin kokari domin taimakawa Najeriya wajen ceto 'yan matan da suka bace, tare da kawo karshen tashe-tashen hankalin da suka ki ci suka ki cinyewa a wasu sassan Najeriya.

Jonathan ya gode da irin taimakon da Amurka za ta bayar, inda ya ce, sojojin Najeriya wadanda yanzu haka suke kokarin neman 'yan matan za su goyi bayan matakan da jami'an tsaron Amurka za su dauka.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China