in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke 'yan bindiga 42 a Najeriya
2013-07-30 15:10:27 cri
Wani babban jami'in soji a kasar Najeriya ya bayyana ranar Litinin cewa an cafke mutane 42 da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne a yankin kudu maso yammacin kasar.

Kwamandan runduna ta 81 ta sojin Najeriya Manjo Janar Obi Umahi ya ce an cafke mutanen ne a jihohin Lagos da Ogun dake kudu maso yammacin kasar tsakanin 12 zuwa 23 ga watan Yuli, bayan mamaya da aka yi bisa rahotannin sirri da aka samu.

Ya kara da cewa, wasu daga cikin wadanda aka cafke sun tabbatar da cewa su 'yan kungiyar Boko Haram ne, kana wasu daga cikinsu, suka yi aikace-aikacen kungiyar a wasu sassan kasar.

Babban jami'in sojan ya ci gaba da cewa, wasunsu suna daga cikin wadanda suka kashe sojoji da farar hula a garin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China