in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar NEMA ta Najeriya ta ce sama da mutane dubu 250 suka rasa muhallansu saboda rikicin Boko Haram
2014-03-30 15:21:17 cri

Hukumar bada taimakon gaggawa ta Nigeriya wato NEMA ta bayyana cewa akalla mutane miliyan uku ne hare-haren 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ya shafa, sannan kuma kusan dubu dari biyu da hamsin suka rasa matsugunansu, a sashen arewa maso gabashin kasar tsakanin watanin Janairu da Maris na wannan shekara.

Shugaban hukumar NEMA Mohammed Sani Sidi ya bayyana hakan a wajen taro na 7 akan yadda ake bada taimako na jin-kai na kasa, da hukumar ta shirya shi a Abuja, babban birnin tarayya.

Alhaji Sani Sidi wanda yayi bayanin a cikin sakon sa wajen taron ya ce, NEMA tare da hadin-gwiwar kungiyar bada agajin jin-kai wato Red Cross da kuma hukummin bada agajin gaggawa na jihohin da abin ya shafa, sun aiwatar da samun bayanai na hakikanin bukatun jin-kai na wuraren da abin ya shafa.

Jami'in mulki Zanna Muhammed wanda ya wakilci shugaban hukumar, ya bayyana cewar an yi wannan tantancewar ne a tsakanin ranar 6 da kuma 7 na watan Maris din shekara ta 2014.

"Rahoto na tantance bukatun da ake da su ya nuna daga watannin Janairu zuwa Maris hare-haren da aka kai , da kuma sauran matsalolin da aka fuskanta, na bukatun taimako na jin-kai, al'amarin da ya shafi fiye da mutum miliyan uku.

Taron kamar yadda Wakilin Shugaban ya kara jaddadawa, an kira shi ne saboda ayi nazari kan irin halin da ake ciki, a jihohin da suke fuskantar hare-haren ta'addanci, da kuma kara samo hanyoyi da zasu bi, sannan su masu bada taimako daga cikin gida da kuma kasashen wajen, su maida himma kwarai da gaske.

Ya ce koda yake dai ita hukumar NEMA ta taimaka wajen bangare bada abinci, da kuma sauran wasu bukatu daban-daban, da suka hada da ruwa da kuma magunguna. Bukatun wuraren kullum karuwa suke, don haka ya bukaci wadanda ke bada taimako da kada su gaji saboda mawuyacin halin da jama'ar da abin ya shafa suke ciki.

'Yan kungiyar nan ta Boko Haram dai sun dauki alhaki na duk hare-haren da aka kai a sashen arewa maso gabashin Najeriya, musamman ma jihohin Borno, Yobe, da Adamawa, wanda a sanadiyyar haka ne, aka yi asarar mutane dubbai tun daga shekara ta 2009, duk kuwa da yake an kafa dokar-ta -baci a jihohin uku. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China