in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mayakan Boko Haram da dama sun mutu sakamakon samame ta sama, in ji rundunar sojojin Najeriya
2013-12-15 16:20:24 cri
Rundunar sojojin kasar Najeriya ta kashe mambobin kungiyar Boko Haram da dama a wani samamen da sojojin kasar suka kai ta jiragen saman yaki, in ji wani babban jami'in sojojin kasar a ranar Asabar 14 ga wata.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya rukuni na bakwai dake birnin Maiduguri, kanal Mohammad Dole ya bayyana cewa, sojojin Najeriya sun kai wani samame ta jiragen sama kan wasu yankunan mayakan kungiyar Boko Haram dake yammacin Maiduguri, hedkwatar jihar Borno, tare da hallaka 'yan ta'adda da dama.

Kanal Dole ya nuna cewa, sojojin Najeriya sun gumurzu na tsawon kimanin sa'o'i biyu tare da 'yan kungiyar a kan hanyar Maiduguri zuwa Bama da Gwoza, a kudancin birnin Maiduguri, tare da kashe 'yan ta'adda takwas da kuma raunana wasu da dama.

Haka kuma jami'in ya kara da cewa, sojojin za su ci gaba da kai samame ta sama kan 'yan ta'adda, wanda ya rage lagon mambobin kungiyar Boko Haram sosai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China