in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Najeriya sun kashe mambobin Boko Haram 20
2013-11-17 17:15:47 cri
Rundunar sojojin tarayyar Najeriya ta kashe wasu mayakan da ake zargi da 'yan Boko Haram a yayin wani samame kan sansanin 'yan tawayen a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar Najeriya tare da lalata motoci da babura 50, a cewar rundunar sojojin a ranar Asabar.

Kakakin reshen rundunar sojojin kasar Najeriya na bakwai, laftanan kanal Muhammad Dole ya bayyana cewa sojojin gwamnati sun kawar da masu ta da kayar baya a cikin wani kazamin samame kan sansanin 'yan kungiyar Boko Haram dake Bita, inda suka kai hare hare kan hanyar dake zuwa Damboa da Gwoza.

Haka kuma jami'in ya jaddada cewa soja guda ya mutu, kuma uku suka jikkata a yayin wannan samame. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China