Wasu wadanda suka ganewa idanunsu yadda lamarin ya auku, sun shaida wa majiyar kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua cewa, harbe-harben da maharan suka yi ya haddasa yamutsi tare da raunata mutane da yawa.
Rahotannin sun kuma bayyana cewa ba a bude manyan kasuwannin dake birnin Yola ba a jiya Jumma'a, sakamakon binciken da jami'an tsaron suke yi domin tsafke wadanda suka aikata wannan ta'asa.
Kawo yanzu dai, ba a tabbatar da ko kungiyar nan ta Boko Haram ce ta kaddamar da wannan hari ba. (Saminu Alhassan)