in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeria ta bukaci taimakon MDD wajen yaki da Boko Haram
2014-03-28 17:03:18 cri
A ranar Alhamis ne Shugaban Majalisar dattawan kasar Nigeriya David Mark ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta shiga tsakani tare da ceto kasar ta Nigeriya daga tashin hankanli da 'yan ta'adda suka yi, wanda ke addabar kasar a halin da ake ciki.

Mark ya gabatar da wannan kira ne a yayin da ya karbi bakuncin mataimakin sakatare janar na MDD Jan Eliasson a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Mark ya ce, kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta yana bukatar goyon baya da tallafi daga majalisar ta dinkin duniya.

Ya kuma jaddada cewar, Nigeriya za ta ci gaba da gudanar da muhimmam ayyuka a harkokin shiyya-shiyya da kuma na duniya baki daya, musamman da yake kasar ta taka rawar da ta dace a ayyuka na samar da zaman lafiya.

David Matrk ya ce, Nigeriya zata ci gaba da daidaita kalubalen da take fuskanta domin samun mafita.

A nasa bangaren, Eliasson ya yaba da Nigeriyar da ta ci gaba da goyon baya da bayar da hadin kai ga majalisar ta dinkin duniya, a inda kuma ya yi alkawari cewar, majalisar za ta dauki mataki na taimakawa Nigeriya wajen murkushe ta'addanci.(Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China