Ranar Jumma'a 25 ga wata, Ban Ki-moon, babban sakataren MDD ya ba da wata sanarwa dangane da cika shekaru 28 da abkuwar bala'in bazuwar tururin nukiliya a tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da nukiliya ta Chernobyl da ke kasar Ukraine.
A cikin sanarwarsa, mista Ban ya ce, MDD ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita kalubalen da mutanen da bala'in ya shafa suke fuskanta, ya zuwa yanzu tana himmantuwa wajen aiwatar da shirinta na rage radadin bala'in. Mista Ban ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su kara nuna goyon baya wajen farfado da wuraren da bala'in ya shafa da kuma tabbatar da samun bunkasuwa mai dorewa a wuraren, su yi amfani da darasi da fasahohin da aka samu sakamakon bala'in wajen daidaita abubuwan da suka biyo bayan abkuwar bala'in nukiliya, tare da rubanya kokarinsu na hana sake abkuwar bala'in nukiliya.
Ranar 26 ga watan Afrilu na shekarar 1986, an samu fashewar wani injin da ke tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da nukiliya ta Chernobyl da ke kasar Ukraine, inda dimbin tururin nukiliya ya bazu, wanda ya zama hadarin bazuwar tururin nukiliya mafi tsanani a duk fadin duniya har zuwa yanzu. (Tasallah)