Kasar Sin ta bayyana cewa, kamata ya yi kasashe masu ruwa da tsaki su jingine manufufin su game da ba da tsaron nukiliya ga kwayen su, su kuma kauracewa yada fasahohin da suka shafi hakan ga wadanda suke so.
A cewar mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying, idan har ana fatan kwance damara dangane da makaman nukiliya, tilas ne a tabbatar da daidaito ga dangantakar kasa da kasa.
Tsokacin na Madam Hua ya biyo bayan tambaya da aka yi mata cewa, mene ne matsayin kasar Sin, game da shawarar da Japan ta gabatar tare da wasu masu ruwa da tsaki cewa, ya dace kasashe duniya ciki hadda Amurka, da Rasha, da Sin, su yi shawarwarin da juna don kwance damarar makaman nukiliya. Madam Hua ta ce, sa kaimi ga yunkurin kwance damarar makaman nukiliya, da samar da wata duniya maras makaman nukiliya, buri ne na dukkan kasashen duniya, kuma kamata ya yi kasashen da ke da makaman nukiliya sun yi kokari sosai domin cimma wannan buri.
Hua ta kara da cewa, har kullum kasar Sin na ganin an haramta, tare da lalata makaman nukiliya, tana kuma aiwatar da manufofin da ke tabbatar da kaucewa amfani da makaman nukiliya.
Kaza lika, Sin ba ta da niyyar amfani, ko barazana ga kasashe da yankunan da ba su da makaman na nukiliya. Ba ya ga kasancewar kasar ta Sin ba ta taba girke makaman nukiliya a ketare ba, kuma tana bayar da muhimmin taimako ga yunkurin kwance dammar makaman nukiliya a dukkanin fadin duniya. (Danladi)