An bude taron kasashe biyar da ke da makamin nukiliya a Litinin din nan a nan birnin Beijing. Taron wanda shi ne irinsa na 5, da kasashen Sin, da Amurka, da Rasha, da Britaniya da kuma Faransa suka gudanar, wannan ne karon farko da Sin ke daukar nauyin shirya shi.
Mataimakin ministan harkokin wajen Sin Mista Li Baodong, ya gabatar da wasu shawarwari biyar, a yayin bikin bude taron, wadanda suka hada da mayar da aikin tabbatar da tsaron nukiliya a fadin duniya, ya zama babban makasudin kasa da kasa. Da kara amincewar juna, da hada kai tsakanin wadannan kasashe biyar. Sauran shawarwarin sun hada da kara sanya hukumomin duniya, kamar MDD da sauransu, su taka muhimmiyar rawa dangane da makaman nukiliya. Sai gudanar da shawarwari bisa daidaito wajen amfani da makamashin nukiliya yadda ya kamata, tsakanin gwamnatocin kasa da kasa, da sauran hukumomin shiyya-shiyya, masu zaman kan su, wajen kokari tare don raya makamashin nukiliya. (Danladi)