An ba da labari cewa, a ran litinin din nan 14 ga wata, aka kai harin bam a wata tashar motor dake wajen birnin Abuja fadar gwamnatin kasar ta Nijeriya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama wassu kuma suka ji rauni.
Madam Hua a lokacin taron manema labarai na duk rana a nan Birnin Beijing ta ce, Sin ta yi Allah wadai da kakkausar murya sannan kuma ta na yaki da ko wani mataki na ta'ddanci,a don haka ne kuma ta bayyana alhinin ta akan wadanda wannan hari ya rutsa dasu kuma ta mika ta'aziyar ta ga iyalan wadanda suka mutu a sanadin harin.
Madam Hua ta nuna cewa, a matsayin babbar abokiyar Nijeriya, Sin za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da gwamnatin Nijeriya take yi na kiyaye zaman lafiya da karko a yankinta. (Amina)