in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron karawa juna sani dangane da yaki da cutar malariya a Legas
2013-04-22 10:58:10 cri

Ranar 25 ga watan Afrilun kowace shekara, rana ce ta yaki da cutar malariya ta kasa da kasa. Albarkacin wannan rana, sashin kula da tattalin arziki da kasuwanci na karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Legas a Najeriya, gami da kungiyar bada agaji ta duniya SOS, sun shirya wani taron karawa juna sani, dangane da yin rigakafi, da yaki da cutar malariya. Ga rahoton da wakilinmu Murtala ya hada mana.






Taron dai ya samu halartar shugaban sashin kula da tattalin arziki da kasuwanci na karamin ofishin jakadancin Sin dake Legas Mista Jiaping, da likitocin kungiyar SOS, tare da wakilai sama da 30 daga kamfanonin kasar Sin dake wurin.

Dokta Ran Longjian daga kungiyar bada agaji ta SOS reshen Legas, shine ya jagoranci taron, inda ya ce, cutar malariya tana addabar mutane da dama a Najeriya, don haka ya zama dole a mayar da hankali sosai kan rigakafin ta. Kamata yayi ma'aikata 'yan asalin kasar Sin dake aiki a Najeriya su kara fahimtar hanyar yaduwar cutar malariya, da yadda za'a sha magani ta hanyar da ta dace, da kuma yin amfani da gidan sauro, da shafa maganin sauro a jiki. Kuma idan aka ga alamun cutar, ya zama dole a je ganin likita ba tare da wani jinkiri ba, kamar dai yadda ya bayyana.

Yayin wannan taro, suma wakilan kamfanonin kasar Sin sun tofa albarkacin bakinsu, dangane da cutar malariya wato zazzabin cizon sauro, inda suka gabatar da tambayoyi da dama.

A nasa bangaren, shugaban sashin kula da tattalin arziki da kasuwanci na karamin ofishin jakadancin Sin dake Legas Mista Jiaping, ya jaddada cewa, hadin-gwiwar Sin da Najeriya ta fuskar kasuwanci na bunkasa cikin sauri, shi ya sa ake kara samun 'yan kasar Sin wadanda suke zuwa Najeriya, don gudanar da ayyuka. Malam Bahaushe dai kan ce, "lafiya uwar jiki". Don haka idan ka ji alamun zazzabi, ya zama dole ka ziyarci asibiti don ganin likita ba tare da bata lokaci ba.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Legas, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China