A hirarsa da wakilinmu a yau Laraba 27 ga wata a nan birnin Beijing, Alhaji Bamanga Tukur ya bayyana fatansa na cewa, za a dauki darasi daga wadannan matakai, a kokarin taimakawa Nijeriya wajen yin kwaskwarima.
Dangane da yin kwaskwarima kan yaki da cin hanci da rashawa, Alhaji Bamanga Tukur ya ce, yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Sin take yi, babban dalili ne na samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar cikin sauri. Don haka shi ma yana fatan jam'iyyar dake rike da mulkin kasar Nijeriya PDP za ta bi hanyar da JKS take bi don horar da membobinta, tare da daukar matakan yin bincike da kansu ko kuma yin binciken juna, a kokarin tabbatar da kyakkyawar dabi'ar jam'iyyar, da sa kaimi ga bunkasuwar kasar baki daya. (Fatima)