in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake yin girgizar kasa a arewacin Chile
2014-04-03 15:47:30 cri
Wasu rahotanni da shafin yanar gizo, na hukumar nazarin yanayin kasa na kasar Amurka ta fitar, na nuna cewa, wata girgizar kasa mai karfin awo 7 da digo 6 bisa ma'aunin Richter ta sake aukuwa, a arewacin kasar Chile.

Hakan dai ya biyo bayan girgizar kasar da karfinta ya kai awo 8 da digo 2 bisa ma'aunin Richter, wadda ta auku a ranar Talata, a yankin tekun dake kusa da birnin Iquique a arewacin kasar ta Chile.

Kawo yanzu dai, ba a samu cikakken rahoto game da yawan mutanen da wannan bala'i ya aukawa ko asarar dukiyoyi ba.

Bayan aukuwar girgizar kasar, sashen da abin ya shafa na Chile ya sanar da gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa da akewa lakabi da tsunami, wadda ka iya shafar mutanen dake zaune kusa da tekun arewacin kasar. Don haka ne ma ofishin ya gaggauta janye al'ummun dake zaune a wannan waje.

A yau Alhamis da safe kuma, an gano igiyar ruwa ta tsunami a yankin tsibiran Japan, da gabar tekun Pacific, daga inda girgizar kasar mai tsanani ta kasar Chile ta taso, wadda tsayin ta ya kai santimita 40, daura da lardin Lwate dake arewa maso gabashin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China