in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi girgizar kasa mai karfin digiri 5.9 bisa ma'aunin Richter a yankin Diqing na lardin Yunnan na Sin
2013-09-01 17:18:10 cri
A ranar Asabar 31 ga watan Agusta, an yi girgizar kasa mai karfin digiri 5.9 bisa ma'aunin Richter a iyakar gundumar Shangri-la da Deqin ta yankin Diqing na lardin Yunnan da gundumar Derong ta lardin Sichuan, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 3, yayin da wasu mutane 36 suka jikkata. Gidaje da yawa sun lalace, tare kuma da lalata wasu manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a fannonin sufuri da samar da wutar lantarki da sadarwa da sauransu. Yanzu ana kokarin gudanar da aikin ceto a wurin.

Bayan abkuwar bala'in, an dauki matakin yaki da girgizar kasa bisa matsayi na uku cikin gaggawa a lardin Yunnan. Hukumar kula da harkokin jama'a ta lardin Yunnan ta kebe tantuna 5000, da gadoji 4000, da katifa 4000, da barguna 8000, da manyan riguna 8000 zuwa yankin Diqing dake fama da bala'in. Ban da haka, ma'aikatar kula da harkokin jama'a ta Sin ta dauki niyyar bayar da tantuna 2000, da barguna dubu 10, da manyan riguna dubu 10 zuwa yankin na Diqing.

Kawo yanzu dai, an riga an ba da jiyya ga wadanda suka jikkata a asibitoci, a cikinsu, guda hudu sun jikkata sosai, amma rayuwarsu ba ta fuskantar barazana. Hukumar kiwon lafiya ta lardin Yunnan ta tura wani rukunin likitoci da wani rukunin kashe kwayoyin cuta zuwa yankin dake fama da bala'in, tare da isassun magunguna da kayayyaki, domin hana yaduwar cututtuka a wuraren da ake fama da wannan bala'in baki daya.

Dadin dadawa, sojoji da 'yan sanda da jami'ai da jama'ar yankin Diqing, dukkansu sun fara aikin ceto, da neman masu fama da bala'in girgizar kasa da kuma jigilarsu zuwa wurare masu tsaro, da yin bincike kan bala'in da sauransu. Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, kawo yanzu mutane sama da 3100 sun riga sun fara aikin ceto a wurin, yayin da mutane da yawa suke jiran ba da agaji a ko da yaushe.

A matsayin wani muhimmin wurin shan iska na lardin Yunnan, an rufe manyan wurare na yawon shakatawa a yankin Diqing a yanzu. Kuma an yanke shawarar jinkirta lokacin fara karatu a duk makarantun dake gundumar Shangri-la da ta Deqin ta yankin Diqing.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China