in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi girgizar kasa mai karfin maki 7.3 bisa ma'aunin Richter a jihar Xinjiang
2014-02-12 21:18:33 cri
An yau ne misalin karfe 5 da mintoci 19 na yamma aka yi wata girgizar kasa mai karfin maki 7.3 bisa ma'aunin Richter a gundumar Yu Tian dake jihar Xinjiang ta Uighur mai ikon cin gashin kanta, daga baya kuwa, an fara samun wasu kananan girgizar kasa wadanda karfinsu har da ya kai maki 5.7. Rahotanni daga wurin na cewa, babu wani babban kauye cikin da'irar da nisanta ya kai kilomita 50 da inda girgizar kasar ta abku. Ya zuwa karfe 7 na daren yau, ba wani mutum da ya mutu ko kuma jikkata sakamakon bala'in ba a wani kauyen dake kusa da wurin, sai dai wasu gidaje sun lalace.

Bayan aukuwar bala'in, shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang sun ba da umurni ga hukumomi da abin ya shafa na wurin da su ba da kulawa ga wuraren dake fama da bala'in da ba da jiyya da aikin ceto cikin gaggawa, tare kuma da sa ido kan bala'in ta yadda za a ba da tabbaci da kare dukiyar jama'a a wurin. An ce ya zuwa karfi 6 da mintoci 30 na yamma, hukumar rage radadin bala'in, ma'aikatar harkokin cikin gida sun mai da martani cikin loakci kan bala'in tare kuma da tura rukunonin ma'aikata zuwa wurin domin taimakawa jihar wajen yaki da bala'in da tsugunar da wadanda suke fama da matsala. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China