Da misalin karfe 8 da mintoci 46 na yamma na ranar 1 ga watan Afrilu bisa agogon wurin, an yi girgizar kasa da karfinta ya kai awo 8 da digo 2 bisa ma'aunin Richter a arewacin kasar Chile. Bayan haka, an sake yin girgizar kasa sau da yawa. Labarai masu dumi-dumi da muka samu daga gwamnatin wurin, an ce, ya zuwa yanzu, mutane 5 sun mutu sakamakon babbar girgizar kasa.
Sabo da cibiyar girgizar kasa tana cikin teku, sakamakon haka ne igiyar ruwa mai karfin gaske da ake kira tsunami ta riga ta rushe bakin teku a Chile, igiyar ruwa da ta kai fiye da tsayin mita 2 da wani abu. Ministan harkokin cikin gidan Chile ya yi nuni da cewa, a cikin awoyi 6 masu zuwa, za a ci gaba da yi wa jama'a gargadi kan babbar igiyar ruwa. A sa'i daya kuma, ya yi gargadi ga mazaunan Chile da su tsaya a cikin yankunan inda babu bala'in, inda suke jiran labarun daga gwamnati.
Kafin haka, hukumar nazarin girgizar kasa ta Chile ta taba yin gargadi kan igiyar ruwa ga Peru da Ecuador da dai sauransu. Amma bayan haka hukumomin da abin ya shafa sun soke gargadin da ake yi wa sauran kasashe ban da Chile da Peru. (Danladi)