Lardunan Cebu da Bohol sun fi fuskantar wannan bala'I mai tsanani. Gwamnatin Philippine ta bayyana a ran 15 ga wata cewa, a halin yanzu masu aikin ceto suna kokarin shiga yankunan da suke fi gamuwa da bala'in da ke tsibirin Bohol. Bala'in ya lalata hanyoyi da gadoji, kuma ya katse wutar lantarki, jiragen sama masu saukar ungulu sun dakatar da aikin dalilin mugun yanayi, lamarin dake kawo fargabar kara samun yawan mutuwar mutane. Bangaren soja na Philippine ya bayyana cewa, yanzu ana kirawo sojoji dake cikin lifi domin tinkarar wannan girgizar kasa.