Sojojin tawagar yaki ta kasar Uganda (UGABAG) za'a jibge su a shiyya ta daya a kasar ta Somaliya dake karkashin kulawar sojojin kasashen Uganda da Burundi, in ji kakakin sojojin Uganda Paddy Ankunda a cikin wata hirarsa ta wayar tarho tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Wadannan sojojin za'a jibge su ta yadda ya dace a wannan shiyya ta daya, kuma za su taimaka wajen karfafa zaman lafiya da tsaro a yankunan da aka barbe daga hannun mayakan kungiyar Al-shebab, in ji mista Ankunda.
Sojojin na Uganda da Burundi, a karkashin tawagar kungiyar tarayyar Afrika dake kasar Somaliya (AMISOM), an jibge su a wannan shiyya ta daya dake kunshe da yankunan Banadir, Bas da Moyen-Shabelle da kuma shiyya ta uku da ta hada yankunan Baie da Bakool. Haka kuma sojojin suna gudanar da aikin sintiri a Mogadiscio, babban birnin kasar da kuma garin Markal. (Maman Ada)