Za a kashe kudaden dalar Amurka 100 don neman visan yawon shakatawa daga ko wace kasa a cikin wadannan kasashe 3, kuma bayan da masu yawon shakatawa sun samu visan, za su samu lokacin ziyara har na tsawon kwanaki 90 a wadannan kasashe 3. A sa'i daya kuma, jama'ar wadannan kasashe 3 za su iya yin amfani da takardar shaida matsayinsu don yin yawon shakatawa a tsakaninsu.
Dunkulewar visan yawon shakatawa gaba daya a wadannan kasashe 3, zai yi amfani wajen kara darajar ayyukan yawon shakatawa na wadannan kasashe 3. Bisa labarin da hukumar raya yawon shakatawa ta Rwanda ta bayar, an ce, akasarin masu yawon shakatawa da suka ziyarci Rwanda da sauran kasashen da ke gabashin nahiyar Afrika sun fito ne daga kasashen Amurka, Birtaniya, da kuma Jamus.(Bako)