in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda ta rufe ofishin jakadanci da ke Sudan ta Kudu cikin gajeren lokaci
2013-12-19 16:31:20 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Uganda Mista Fred Opolot ya bayyana a ran 18 ga wata cewa, gwamnatin kasar Uganda ta rufe ofishin jakadancinta da ke birnin Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu, sakamakon rikicin da ake samu a makwabciyarta. Uganda ta dauki wannan mataki har sai kura ta lafa a wannan kasa kafin ta sake bude ofishin jakadancinta. A halin yanzu, ma'aikatan ofishin jakadancinta dake kasar ta Sudan ta kudu suna zaman jiran umurni daga gwamnatin kasarsu, idan kuma halin da ake ciki a wannan kasa ya kara tsanacewa, gwamnatin Uganda za ta bukaci jama'arta da su janye daga Sudan ta Kudu ba tare da bata lokaci ba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China