in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarayyar Turai ta jinjinama Uganda bisa ga kokarinta na samar da zaman lafiya a Sudan ta kudu da Somaliya
2014-02-16 16:34:30 cri
Babban jami'in diplomasiyya mai kula da nahiyar Afrika na kungiyar tarayyar Turai EU Nicholas Westcott ya jinjina ma Uganda domin kokarin da take yi na ganin an samu zaman lafiya a Sudan ta Kudu da Somaliya.

A wata sanarwa daga fadar gwamnatin Uganda ta bayyana cewa Mr Westcott yayi jinjinar ne lokacin da ya gana da Shugaban kasar Yuweri Museveni a ranar jumma'ar nan.

A jawabin da Shugaba Musevini ya yi ma bakon na shi ya ce yaki a kasar Sudan ta Kudu zai kawo babban illa akan tattalin arzikin Uganda idan ba'a shawo kan shi ba cikin lokaci kuma yana matukar farin cikin ganin an samu sassauci sannan hada hadar kasuwanci na farfadowa yadda aka so.

Kasar Uganda dai ta aika da sojoji a kasar Sudan ta kudu domin hana abin da ta kira alamun kisan kare dangi dake kunno kai, ta kuma aika da sojojinta zuwa Somaliya.

Nicholas Westcott ya dai gayyaci Shugaba Yuweri Musaveni zuwa ga taron kungiyar Tarayyar Turai da Afrika da za'a yi tsakanin ranakun 2-3 ga watan Afrillu mai zuwa a birnin Brussels. Taron dai Shugaban EU Van Rompuy da Jose Manuel Barroso shugaban kwamitin Turai ne zasu shirya shi tare da shugaban kungiyar Tarayyar kasashen Afirka AU bisa taken zuba jari a al'umma,cigaba da zaman lafiya. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China