in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kyautata shirinta na binciken jirgin saman Malaysiyan da ya bace
2014-03-16 17:00:39 cri
A daren jiya Asabar 15 ga wata ne ministan sufuri da jigilar kayayyaki na kasar Sin, Yang Chuantang, ya kira wani taro a karo na 14, na shugabannin shirin gano inda jirgin saman kasar Malaysiyan nan ya shiga, inda aka bayyana kudurin ci gaba da kokarin aikin laluben jirgin, ciki hadda batun canza wuraren da ake bincike, aikin da cibiyar aikin ceto a yankin tekun Sin za ta kyautata.

Sakamakon sabbin sakwannin da Malasiya ta gabatar, cibiyar aikin ceto a yankin tekun kasar ta Sin tana kara tabbatar da hakikanin bayanai kan wannan batu, tare da hukumar aikin ceto a yankin tekun Malaysia. Ciki hadda shirin amfani da jiragen ruwan Sin, wadanda zasu yi aiki da ya dace da halin da ake ciki.

Kafin hakan a yammacin jiya Asabar, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, Xie Hangsheng yayi wata ganawar gaggawa da jakadan Malaysia, Iskandar Sarudin, inda Xie ya furta cewa, gwamnatin Sin da jama'arta, suna maida hankali kwarai da gaske, kan sabbin sakwannin da Malaysiya ta gabatar a ranar 15 ga wata. Kuma an kira taron gaggawa domin yin nazari kan wannan batu, inda aka yanke shawarar kira ga Malaysiyan, da ta kara azamar aikin ceto, da yin hadin gwiwa da Sin kan batun kyautata tsarin aikin laluben wannan jirgi, da ci gaba da bayar da sakwanni ga Sin a dukkanin fannoni.

Ban da haka Xie ya kara da cewa, har yanzu babu wata masaniya kan inda wannan jirgin saman yake. Iyalan fasinjoji Sinawa dake cikin jirgin dai suna ci gaba da nuna damuwa matuka. Don haka ya Kamata, Malaysiya ta kwantar da hankalin 'yan uwan fasinjojin yadda ya kamata.

A wani ci gaban kuma, masanan kasar Sin sun tashi zuwa Malaysia a daren na jiya, domin shiga aikin hadin gwiwa da wakilan gwamnatin Malaysiya. Ana kuma fatan Malaysiyan za ta ci gaba da nuna goyon bayanta yadda ya dace, in ji mataimakin ministan.(FATIMA)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China