"Na amince sosai da sakamakon da aka samu a kasar Burundi a shekarun baya baya a fannin siyasa, zaman lafiya da kuma tattalin arziki tare da wannan tsarin cigaba wanda tuni ya kawo alfanu a fannoni da dama" in ji mista Rongier.
"A shirye muke na taimakawa mutanen kasar Burundi, domin muhimmin lokaci na tarihin kasar, lokaci ne na kara rubanya kokari domin aza kasar bisa hanyar bunkasuwa da kuma shiga cikin tattalin arzikin shiyyar, tsakiyar Afrika da ma gabashin Afrika" ya shaida wa manema labarai.
Hakazalika ya yi alkawarin ba da tallafin kudi ta yadda gwamnatin kasar Burundi za ta iya samun damar biyan ma'aikatanta cikin lokaci kuma yadda ya kamata, haka kuma da samar da kudade wajen bunkasa ayyukan samar da makamashi, da kuma dunkulewar kasar tare da sauran kasashen shiyyar ta hanyar layin dogo wadda zata taimakawa wajen jigilar karfen nickel na Musongati dake gabashin kasar Burundi.(Maman Ada)