Tuni aka dauki matakan da suka wajaba a wadannan yankunan kasar Rwanda domin kaucewa da ma yaduwar wannan cuta mai kashewa musamman ma a yankunan dake kan iyakokin kasashen biyu dake nahiyar Afrika ta tsakiya, a cewar wakilin minista Bonaventure Nzeyimana.
A cewar rahotannin, annobar kwalara dake cin karanta ba babbaka a cikin makonni ukku na baya bayan nan a kasar Burundi ta yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane hudu yayin da mutane fiye da 400 suke dauke da nau'in cutar a arewacin wannan kasa dake raba iyaka da kasar Rwanda.
Sai dai kuma ma'aikatan likitoci suna danganta wannan annobar kwalara da rashin matakan tsabta dake da nasaba da rashin ruwan sha masu tsabta da kuma rashin kyautatuwar muhalli.(Maman Ada)