Mai kula da harkokin watsa labarai na HCR a kasar Burundi, mista Bernard Ntwari ya ce, a kasar Burundi, hukumar HCR na bada kariya da taimako ga kusan mutane 48,508 da suka hada da 'yan gudun hijira da masu neman mafaka, inda 24,074 aka rarrabasu a cikin sansanonin Gasorwe, Musasa da Bwagiriza, sannan kuma fiye da 250 a sansanin Butare, kana kuma 24,436 a yankunan birane.
Haka zalika ya bayyana cewa tun a shekarar 2002, HRC ta taimaka wajen komawar 'yan gudun hijirar kasar Burundi kusan 515,070 cikin kasarsu kana kuma HCR ta nuna himma wajen bada taimako ga mutanen da suka kaura zuwa wasu yankunan kasar.
'Yan gudun hijiar kasar Burundi na baya baya an kiyastasu a fiye da 38,300 da suka samu mafaka a kasar Tanzania a cikin sansanin 'yan gudun hijira na Mtabila, ana shirin maido a kasarsu nan da karshen shekara.
Sansanonin Musasa da Bwagiriza sun kasance a yankunan Ngozi dake arewa da Ruyigi dake gabas, kana sansanin Butare na cikin yankin Rutana dake kudu maso gabas. Kuma dukkansu na dauke da 'yan gudun hijira 'yan asalin kasar Congo-RDC. (Maman Ada)