in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmanci hadin kai tsakanin al'umma
2014-03-04 20:53:17 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci tattaunawa a zauren taro karo na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC ta 12, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan al'umma.

A cikin jawabin sa ga mahalartan taron,Shugaba Xi ya jaddada muhimmancin dake akwai ga jama'ar kasar Sin su kare halin siyasa da ake ciki na samun hadin kai tsakanin al'umma, tare kuma da yaki da ko wani mataki da zai kawo akasin hakan, ta yadda dukkan al'umma zasu hada kai cikin dogon loakci da tabbatar da zaman karko na al'umma har da tabbatar da dinkuwar kasar.

Mr Xi ya nuna cewa, aikin kiyaye hadin kan al'umma na da muhimmanci sosai don haka ya kamata a nace ga bin tsarin musamman na gurguzu na kasar Sin, wadda ta zama hanya ta siyasa, kuma kamata ya yi a rike hanyar domin tabbatar da aikin al'umma cikin sabon hali.Shugaban ya kara da cewa, ya kamata, a tabbatar da manufar al'umma don kara samun amincewa daga kananan kabilu kan fannoni daban-daban ciki hadda hukumar kasa, al'umma, al'adu, tsarin gurguzu na musamman na kasar Sin. Ban da haka,inji shi ya kamata a sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin al'ummar kananan kabilu, ta yadda jama'ar wadannan wurare za su ci gajiya yadda ya kamata. Hakazalika ya ce, yin hadin kai yana da muhimmanci sosai, domin kawo baraka zai jawo illa ga daukacin al'ummar kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China