An shirya taron share fagen taron shekara-shekara, na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, a ranar 4 ga watan nan da safe, a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin.
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar Mista Zhang Dejiang, shi ne ya jagoranci bude taron. A gun taron, an zabi tawagar shugabanni, da babban sakataren taron na wannan karo.
Bisa ajandar taron da aka zartas, za a saurari, tare da dudduba rahoton da aka tattara kan aikin da gwamnati take gudanarwa a gun taron, za kuma a dudduba, a amince da halin da ake ciki, wajen aiwatar da shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a shekara ta 2013, da daftarin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma na shekara ta 2014.
Har ila yau ana sa ran amincewa da shirin raya tattalin arziki, da zamantakewar al'umma na shekara ta 2014, za a kuma dudduba, tare da amincewa da halin da ake ciki wajen gudanar da shirin kasafin kudi, na gwamnatin tsakiya ta gwamnatocin larduna na shekara ta 2013, da na gwamnatin tsakiya na shekara ta 2014.
Ana kuma dai sa ran dudduba rahoto kan aikin zaunannen kwamitin majalisar, da sauraro gami da dudduba rahoton aikin kotun jama'a ta koli, da aikin babbar hukumar bin bahasi ta jama'a. (Danladi)