in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manema labarai na gida da na kasashen waje sama da dubu 3 za su halarci taruka biyu na kasar Sin.
2014-03-02 16:27:03 cri

Rahotanni daga cibiyar watsa labaru ta taro karo na biyu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 da taro karo na biyu na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na Sin na 12 na nuna cewa, 'yan jarida na gida da na kasashen waje sama da dubu 3 sun yi rajistar gudanar da ayyukan su a gun tarukan biyu.

Bana shekara ta farko ke nan ta tabbatar da sakamakon da aka samu a gun cikakken taro karo na 3 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 18. Wakilinmu ya yi nazarin cewa, cikin makwanni biyu masu zuwa, kafofin yada labarai na Sin da na ketare za su mai da hankali sosai kan bunkasuwar tattalin arzikin Sin da kalubalen da za ta fuskanta, da mai da hankali kan yadda za a gudanar da cikakkun matakai na zurfafa yin kwaskwarima a kasar, da kiyaye muhalli, da yin kwaskwarima ga zamantakewar al'umma da ba da tabbaci ga rayuwar jama'a, da yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.

Mataimakin darektan cibiyar watsa labaru na taruka biyu, mista Zhong Xuequan ya yi bayanin cewar "Taruka biyu za su mai da martani ga bukatun jama'a. Za a yi shawarwari kan batutuwan da suka fi jawo hankalin jama'a, domin mai da martani ga bukatun kafofin yada labarai na Sin da na ketare."

Bisa labarin da aka bayar, an ce, cibiyar ta bude shafin watsa labaru a shafin yanar gizo na taruka biyu tun daga shekarar 2006, daga bisani an ba da amsoshin intabiyu ga manema labarai ta sakon tafi da gidan ka na SMS.

A bana an kara da bude shafi ta Wechat, ta yadda 'yan jarida za su sami sakwannin tambayoyin su cikin lokaci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China