A lokacin taron, mambobin majalissar fiye da 2000 za su saurari tare da tattaunawa kan rahoton majalisar gudanawa ta CPPCC da kuma rahoton yadda aka gudanar da ayyuka da aka tabbatar a cikin taro na farko na majalisar CPPCC.
An ba da labari cewa, gidan rediyon CNR, babban gidan telibijin na kasar Sin CCTV da gidan rediyon kasar Sin CRI za su gabatar da shirin kan bikin bude taron da rahoton da Yu Zhengsheng, shugaban majalisar, zai gabatar kan majalisar CPPCC kai tsaye, ban da haka, wasu manyan shafunan yanar gizo na Internet na kasar Sin za su gabatar da shiri kan taron. (Amina)